On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Yan Bindiga Sun Harbi Limami Tare Da Garkuwa Da Masallata A Jihar Katsina

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Maigamji dake karamar hukumar Funtua a jihar Katsina a lokacin da ake gudanar da sallar magariba da masu ibada suka gudanar da sallar Isha’i.

Wani tsohon kansila a mazabar Maigamji a karamar hukumar Funtua ta Katsina, Alhaji Lawal Maigamji, ya ce ‘yan bindigar sun bude wuta kan limamin da yake jagorantar sallar, Malam Yusha’u da wani Hussaini Jamo.

Yanzu haka dai dukkannin mutanen  biyun suna kwance  a wani asibiti dake Funtuwa.

‘Daya daga cikin masallatan  ya tabbatar da cewa anyi garkuwa da mutane 18  yayin harin, inda ya kara da cewa hudu daga cikin wadanda aka sace sun tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su a lokacin da suke tafiya.

A wani harin kuma na daban, bayanai sunce anyi garkuwa da mutane 31 a kauyukan Karare da Kokiya da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah domin jin ta bakinsa, ya ce zai tuntubi baturen ‘yan sanda  na yankin kafin yin karin haske akai.