On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta A Oyo

Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban Makarantar Firamare ta Nomadic da ke Igbojaye, Budo a ƙaramar hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo, Kolawale Mathew Owoade, mai shekaru 60.

Rahotanni sun bayyana  cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar tsakanin ƙarfe biyar zuwa shida, inda masu garkuwar suka nemi a biya su kuɗin fansa na naira miliyan 30.

Ɗansa, Abiola Owoade, ya ce mahaifinsa na kan hanyarsa ta dawowa daga gonarsa da ke Budo Aare lokacin da maharan suka tare shi. Ya ƙara da cewa masu neman sa sun gano baburinsa cikin daji a ranar Lahadi.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar Oyo, Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami'an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto shugaban makarantar.

 

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thunder storm

    High: 33°C | Low: 23°C