On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Yan Bindiga Sun Sace Wani Basarake A Jihar Kogi

Yan Bindiga

Yan bindiga suka yi dirar mikiya fadar Basaraken Oghara dake karamar hukumar Kabba Bunu a jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da basaraken yankin.

Kazalika maharan sun tafi  da wasu manyan  hadiman  basaraken  wadanda  suka hada David Obadofin  da kuma wani mai suna Temidayo  Elewa, a lokacin da suka kai harin.

Bugu da kari maharan  sun bindige  wata  ‘yar aikin gida da suka  tarar  a fadar  sarkin mai suna  Toyin Onare.

Da  yake tabbatar da faruwar  lamarin, Mai magana da  yawun rundunar  ‘yansandan  jihar, SP William Aya,Ya  ce  ‘yan bindigar  sun farwa  fadar  basaraken  ne  da  karfe ukku  na dare,inda suka fara yin harbi a sama, kafin su kaiga  kutsawa  cikin fadar  sarkin.

Ya kara da cewar  a yanzu haka  kwamishinan yansandan  jihar  Hakeem  Yusuf  ya  tura  tawagar  jami’an  yansanda  ta musamman zuwa  yankin da abun ya faru, domin kubutar da  mutanen.