On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

'Yan Bindiga Sun Sace Wani Dan Kasuwa A Karamar Hukumar Rogo

YAN BINDIGA

A jiya ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wani shahararren dan kasuwa, mai suna Alhaji Nasiru Na’ayya dake kauyen Gangarbi a karamar hukumar Rogo tan an jihar Kano.

Wani  ganau wanda  ya bukaci a sakaye sunansa  shine  ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan dan kasuwar ne da misalin karfe 12 na dare, inda suka rika harbin iska kafin su tafi da Dan kasuwar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yana dakon samun cikakken  labarin abunda  ya faru  daga wajen baturen  yansanda  na karamar  hukumar  ta Rogo.