On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Yan Bindiga Sun Sako Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Nasarawa Da Suka Sace

KWAMISHINAN YADA LABARAI NA JIHAR NASARAWA

‘Yan Bindiga sun sako Kwamishinan yada labarai da Raya al’adu da kuma yawon bude ido na jihar Nasarawa Yakubu Lawal bayan da suka yi garkuwa dashi.

Kakakin rundunar yansandan jihar  DSP Ramhan Nansel, shine ya tabbatar da haka ga manema Labarai a Lafiya babban birnin jihar Nasarawa

Idan ba’a manta ba wasu ‘yan bindiga sun yi sace  Kwamishinan ne a gidansa da ke yankin Eggon na  karamar hukumar Nassarawa da yammacin ranar Litinin.

Ya  kara da cewa  Kwamishinan ya kubuta daga hannun masu garkuwar ne a jiya, kuma tuni ya koma wajen iyalansa.

Sai dai ya ce ba a kama wanda ake zargi da yin garkuwa da  kwamishinan Yada Labaran ba, a yayin da jami’an Yansanda ke kara matsa kaimi  domin cafko yan bindigar.