On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Injiniya Salamatu bayan Raba Kayan Tallafi a Jihar Kaduna, sun Bukaci Milliyan 100 Kudin Fansa

Wata majiya daga Iyalan ta fadawa jaridar Daily Trust cewa ‘yan bindigar...

‘Yan bindiga da suka yi garkuwa da Ramatu Abarshi da ‘yar ta da kuma direban motar da suka dauka haya a Kaduna, sun nemi Naira milliyan 100 amatsayin kudin Fansa.

Anyi garkuwa da mutanen uku a kan hanyarsu ta komawa gida daga garin Mariri na karamar hukumar Lere bayan gudanar da wasu ayyukan jin kai inda Injiniya Abarshi ta raba kayyakin amfanin yau da kullum ga magidanta gabanin Idin karamar Sallah.

Wata majiya daga Iyalan ta fadawa jaridar Daily Trust cewa ‘yan bindigar sun tuntubi ‘yan uwan mutanen inda suka nemi a biya Naira milliyan 100 kafin sakin Injiniya Ramatu da ‘Yar ta.

Injiniya Ramatu Tsohuwar Shugabar  Sashen Injiniyancin Lantarki ce a kwalejin Fasaha ta Kaduna.

More from Labarai