On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mutane 44 Cikin Dare A Jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun sace akalla mutane 44 daga kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito, Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun afkawa garin cikin dare, inda suka rika bi gida-gida suna yin garkuwa da mazauna yankin, galibinsu mata da kananan yara.

A baya-bayan nan, an samu kwanciyar hankali bayan an shafe shekaru ana kai munanan hare-hare a kan a garuruwan kananan hukumomin yankin, amma hare-hare da garkuwa da mutane sun sake kunno kai, lamarin da ya sa mazauna garin suka sake zama cikin firgici.

Ana kyautata zaton wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga ne da ake kira Dankarami shine ya yi garkuwa da mutanen.

Har yanzu ‘yan bindigar ba su kai ga kira ‘yan uwan ​​wadanda aka sace ba domin neman kudin fansa.

Ba’a samu ji tab akin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.