On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Tsohon Mataimakin Gwamna A Jihar Nasarawa

Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa farfesa Onje Gye Wado


Mai Magana da yawun rundunar yansandan jihar Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar al’amarin ta cikin wata sanarwa da aka fitar da safiyar yau a lafiya.

Gye Wado wanda ya kasance mataimakin gwamna a tsakanin shekarar alif dari tara da casa’in da tara zuwa shekarar 2003 karkashin gwamnatin Alhaji Abdullahi Adamu.

Tsohon mataimakin yasha sallake yunkurin masu garkuwan kafun wannan al’amarin ya faru a yau.
Mai Magana da yawun rundunar ya kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar Maiyaki Muhammad Baba ta cikin wata sanarwa da aka fitar yace an aike da jami’an tsaro domin ceto tsohon mataimakin gwamnan.