On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

'Yan Boko Haram Sun Kai Sabon Hari Garin Chibok Na Jihar Borno

Garin Chibok da ke jihar Borno ya sake shiga sabon labari bayan wani kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai a yammacin ranar Talata, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

Garin Chibok ya kasance karon farko a labaran duniya a cikin watan Afrilun 2014, lokacin da mahara suka afkawa  makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati tare da sace dalibai sama da 300.

A cewar wani mazaunin yankin, Moses Adamu, harin na baya-bayan nan ya faru ne da misalin karfe 7 na dare, inda nan take ‘yan ta’addan suka afkawa al’ummar garin suna harbe-harbe, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin rudani da gudin tsira da rai.

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce ya samu daukin gaggawa daga rundunar hadin gwiwa, kuma al-amura sun koma dai-dai.