On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

'Yan Chanji Sun Tafka Asara Sakamakon Karyewar Dollar A Najeriya Yayinda CBN Ke Cigaba Da Shirin Sauya Fasalin Naira

Masu harkokin Chanji a jihar Adamawa na kin amincewa da kudaden kasashen waje daga abokan hulda  saboda rashin tabbas da ake samu a kasuwar ta bayan fage.

Wasu ’yan kasuwar da aka zanta da su a Kasuwar Zamani ta Jimeta da ke Yola, sun bayyana cewa sun damu matuka da faduwar dala wanda hakan ya gurgunnta kasuwar hada-hadar. 
Shugaban kungiyar dillalan canji a jihar Adamawa, Lawan Mai Yasin, ya ce ‘yan kasuwar sun yi asara sosai bayan da suka sayi dala a kusan Naira 870 kafin nan take ta fadi zuwa Naira 680. 
Hakan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da shirin na sake fasalin kudin Naira, inda a karshen mako babban bankin Najeriya CBN ya yi alkawarin kare ‘yan Najeriya a yankunan da ba su da  banki da  da marasa amfani da asusun da  kuma yankunan karkara.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na  CBN, Osita  Nwanisobi, ya sanyawa hannu,  babban bankin yace  yana hada gwiwa da hukumomin da abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar hada-hadar kudi don tabbatar da cewa ba a tauye hakkin ‘yan kasa masu rauni ba.

Bankin ya ba da tabbacin cewa an samu wasu ci gaba kamar  kara yawan adadin kudaden da ake ajiyewa a bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi.