On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

‘Yan Fashi Da Makami Sun Harbe Ma’aikacin Makarantar Sakandire A Jihar Nasarawa

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani ma’aikacin Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke karamar Hukumar Nasarawa Eggon a Jihar Nasarawa, Auta Nasela.

Al’amarin ya faru ne da karfe 8:45 na dare a karshen mako inda ‘yan bindigar suka farwa harabar makarantar inda suka je gidan marigayin domin  neman kudi.

Rahotanni sunce  Nasela ya gudu zuwa wani gidan makwabcinsa, inda maharani suka harbe shi har sai da ya mutu. Shi ma wani ma’aikacin makarantar, Timothy Malle, an harbe shi, amma ya tsira daga harin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce al’amarin harin ‘yan  fashi da makami ne.