On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Yan Kwankwasiyya Na Cigaba Da Addu'oin Neman Nasara A Shari'ar Zaben Gwamnan Kano

‘Daruruwan ‘yan Kwankwasiyya ne suka taru a sassan jihar Kano ranar Alhamis domin gudanar da addu’o’i na musamman na neman samun nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a kotun sauraron kararrakin zaben Gwamna.

Yayin da kotun za ta yanke hukunci kan karar zaben gwamna nan ba da dadewa ba, ‘yan Kwankwasiyya na neman daukin Ubangiji  akan shari'ar.

Sallar wacce ta kunshi mabiyan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso, an gudanar da ita ne a titin zuwa  Zaria da Maiduguri da Titin zuwa  Hadejia da titin Gwarzo wadanda su ne manyan hanyoyin shigoea birnin Kano.

Da take jawabi a daya daga cikin wuraren addu’o’in, shugabar kungiyar mata ta NNPP ta jihar Kano, Hajia Zuwaira Abubakar ta ce suna addu’ar neman tsari  daga wadanda suka kuduri aniyar tsige Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.