On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Yan Majalisar Da Kotu Ta Sauke Kan Kujerunsu Sun Ce Zasu Koma Kujerunsu A Yau

PILATO

‘Yan majalisar dokokin jihar Filato 16 da Kotun daukaka kara ta sauke daga kan kujerunsu a watan Nuwambar shekarar data gabata, sun lashi takobin shiga zauren majalisar dokokin jihar a yau, domin cigaba da gudanar da aiyukansu, kamar yadda suka baiyanawa manema Labarai a jiya.

Idan ba’a manta ba,  Kotun daukaka kara ta soke zaben ‘yan majalisun 16 na jam’iyyar PDP  saboda rashin yin aiki  da tsarin da jam’iyya  ta shimfida wajen fitar da ‘yan takara. Haka zalika kotun  daukaka karar  ta soke zaben wasu  ‘yan majalisun dokokin tarayya da  kuma na gwamnan jihar Caleb Mutfwang.

To sai dai Kotun koli  ta jingine hukuncin da kotun daukaka karar  ta yanke akan kujerar gwamnan jihar a ranar  12 ga watan da muke ciki, wanda ta nuna cewar kotun baya  ta yi kuskure a  hukuncin da ta yanke.

Bayan sanar da hukuncin kotun kolin ne, Yan majalisar ta bakin mai magana da yawunsu, Ishaku Maren,  suka yi ikirarin cewar  hutu kawai suka je, kuma yau zasu koma  bakin aiki.