On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Yan Majalissar Dokokin Jihar Rivers Da Suka Sauya Sheka Sun Kawar Da Yiyuwar Sake Komawa PDP

'Daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers su 27 da suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC,  Enemi Alabo George, ya ce dukkansu ba su da wani shiri na sake komawa PDP.

Da yake magana a wani gidan talabijin a daren jiya, dan majalisar ya kuma ce gwamna Siminalayi Fubara ya sanya hannu kan kudurin mai dauke da batutuwa takwas a fadar shugaban kasa a ranar Litinin.

Hakan dai ya sabawa rade-radin da ake cewa bai sanya hannu akan takardar ba, inda ya kara da cewa gwamnan ma ya yi jawabi bayan ya sanya hannu.

George wanda shi ne shugaban kwamitin yada labarai na majalisar ya dage cewa akwai rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP kuma babu gudu babu ja da baya kan shawarar da suka yanke.