On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Yan Majalissar Dokokin Najeriya Na Shirin Katse Hutu Domin Amincewa Da Kasafin 2024

Majalisar dattawa za ta zartas da kudurin kasafin kudin shekarar 2024 a ranar asabar 30 ga watan Disamba don dorewar tsarin kasafin kudin kasa dake farawa daga watan Janairu zuwa Disamba na kowacce shekara.

Jagoran  Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele ya bayyana haka a wata zantawa da ‘yan jarida a garin Iyin-Ekiti na jihar Ekiti a lokacin hutun Kirsimeti, inda ya ce duk ‘yan majalisar tarayya zasu rage hutun su domin ganin an gaggauta amincewa da kudirin kasafin kudin.

A karshe ya bayyana cewa dukkan ma’aikatu da hukumomi za su bayyana a gaban zaman hadin gwiwa na dukkanin kwamitocin da abin ya shafa na majalisar dattawa da  wakilai.