On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Yan Najeriya Dubu 56 Ne Ke Yin 'Kaura Zuwa Kasashen Waje A Kowace Shekara

YAN NAJERIYA

Rahotanni na baiyana cewa wasu ‘yan Najeriya na yin kaura zuwa kasashen waje yayin da adadin fasfo din da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ke bayarwa ya karu da kashi 38 cikin 100 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021.

Binciken ya nuna cewa  hukumar ta bayar da fasfo dubu    767 da 164  a shekarar  2020, amma a shekarar  2021 sai da ta bayar da fasfo milyan 1 da dubu 59 da 607.

Bayanan da aka samu daga hukumar ta  NIS, sun nuna cewa, daga cikin adadadin da aka  bayar, fasfo  444  kadai suka kasance na jami’an gwamnati.

Har ila yau, wani bincike na Bankin Duniya ya nuna cewa ‘yan Najeriya  dubu 56,000 ne ke barin kasar nan a duk shekara.