On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Yan Najeriya Sama Da Dubu 40 Ne Ke Mutuwa Kowacce Shekara Saboda Hadari

Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa, Ta ce sama da mutane Dubu 40 ne ke mutuwa a Najeriya a duk shekara, sakamakon hadurran ababen hawa daban daban a kasar nan.

Wani babban jami’i  a hukumar,  Dauda Biu  ne ya  bayyana haka jiya  a  Abuja, yayin gudanar da bukukuwan makon kare afkuwar   hadurra na Majalisar Dinkin Duniya karo na 7.

Ya kuma ce mutane miliyan 1 da dubu dari  3 ne ake kashewa ke mutuwa  a  kowace  shekara a  fadin  duniya, sakamakon afkuwar  hadurra.

A cewarsa, Babbar  barazanar  dake  tattare  da hadarin tafi  ritsawa da   mutane  dake tsakanin  shekara 5 zuwa  29 .