On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Yan Najeriya Sama Da Milyan 1 Ne Suka Ci Gajiyar Shirin Rage Fatara A Nigeriya

Osinbajo

Mutane milyan daya da dubu dari takwas ne suka amfana da shirye-shiryen.

Gwamnatin tarayya ta ce mutane miliyan 1 da dubu dari 8 ne suka ci gajiyar ayyuka da shirye-shiryen da aka yi a karkashin shirin rage talauci na kasa tare da dabarun bunkasa   cigaban kasa.
A  jiya ne aka  gabatar da rahoton yadda aka gudanar da shirye shiryen  a  Abuja  a yayin wani taro  da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Rahoton ya ce, an yi   shirye-shirye   har guda 100 karkashin shirin bunkasa noma domin  samar da abinci da ayyukan yi da kuma  gina hanyoyin karkara.
Kakakin mataimakin shugaban kasa Laolu Akande, ya ce rahoton ya nuna cewa kananan manoma miliyan 1 da dubu dari 6 ne suka amfana  da tsare tsaren da gwamnatin ta aiwatar.