On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

'Yan Najeriya Sama Da Milyan 24 Ke Fuskantar Barazanar Yunwa

Wani rahoton hadin gwiwa da shirin bunkasa samar da Abinci na Duniya da kuma Hukumar samar da Abinci da bunkasa aikin gona ta Majalisar dinkin duniya suka fitar, ya ce sama da ‘yan Najeriya miliyan 24 da dubu dari 8 na fuskantar barazanar karancin abinci tsakanin watan Yuni da Agusta.

Rahoton wanda aka wallafa shi a ranar Litinin ya bayyana  kasashen  Najeriya da  Afghanistan da Sudan ta Kudu a cikin kasashe 18 da ke fama da yunwa a duniya.

Rahoton ya ce dukkan wuraren da aka zaiyana suna  da tarin jama’a  dake  cikin matsalar rashin abinci, ko kuma suke fuskantar samun matsalar.

Rahoton ya ce,  ana sa ran  za’a iya fuskantar  karuwar  matsalar karancin  rashin abinci a Najeriya  nan gaba, sakamakon matsalar tsaro da ake fama da ita, tare da raunin tattalin arziki da kuma  kalubalen sauyin yanayi.