On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Yan Najeriya Sun Kashe Sama Da Tiriliyan 2 A Kiran Waya Da Sayen Data Cikin Watanni 9

Yawan kudin da jama’ar kasar nan suka kashe a bangare kiran waya da kuma siyan Data ya karu da kimanin naira Tiriliyan 2 da bilyan 59 a cikin watanni 9n farko na shekarar da muke ciki.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa  da kanfanonin sadarwa na MTN Nigeria da Airtel Africa suka fitar.

Hakan ya nuna cewar an samu karuwar kaso  32  da digo  57 cikin 100 daga adadin kudin da aka kashe  a irin wannan tsuki na  shekarar bara, wanda  ya kama naira tiriliyan 1 da bilyan 95.

Yawan  karuwar kudin da ake kashewa wajen kiran waya da kuma  na Data  nada alaka  da yadda aka samu  karuwar masu amfani da Data da kuma  karyewar darajar Naira.