On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Yan Sanda A Jihar Kano Sun Bukaci A Kauracewa Zanga-Zanga Bayan Hukuncin Kotun Daukaka Kara

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi kira ga al’umma  su kwantar da hankulansu, su kaucewa shiga duk wani nau’i na haramtaccen  taro, ko zanga-zanga, ko tattaki da ka iya haifar da tarzoma.

Rundunar, a cikin wata sanarwa da kakakinta, Haruna Kaiyawa, ya fitar, ta ce sahihin bayanai da ke hannunta, sun ce wasu kungiyoyin magoya bayan wata jam’iyyar siyasa na amfani da kafafen yada sada zumunta, suna tara jama’a da shirin fitowa kan  tituna domin nuna adawa da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan, Mohammed Usaini Gumel, ya yi kira ga daukacin al’ummar da su kwantar da hankalinsu, su guji duk wani nau’i na taro, ko zanga-zanga, ko Tattaki.

Ya ce duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a Jihar za a kama shi kuma zai  fuskanci fushin doka.