On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

'Yan Sanda Sun Bankado Wani Shirin Kona Gidan Gwamnatin Jihar Kano

Rundunar ‘yan sanda, ta ce ta gano wani shiri na kona gidan gwamnatin Kano da wasu bata gari ke kitsawa a kan shari'ar da ake ci gaba da yi a kotun koli kan zaben gwamna tsakanin jam’iyyar NNPP da APC.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wani taro da shugabannin kafafen yada labarai, gabanin zaman kotun koli na daukaka kara kan shari'ar kujerar gwamnan Kano da aka shirya gudanarwa yau Alhamis 21 ga watan Disamba 2023 a Abuja.

Gumel ya bukaci kwararrun kafafen yada labarai da su sanar da jama’a yadda ya kamata a kan abubuwan da ke faruwa bisa tsari da gaskiyar labari.

A cewarsa bai kamata a samu tashin hankali a Kano ba domin maganar tana kotun koli da ke Abuja ba a jihar ba.