On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Yan Sanda Sun Cafke Wata Bazawara DaTayi Garkuwa Da 'Yarta A Kano

CP GUMEL

Rundunar yansandan jihar Kano ta cafke wata Bazawara mai suna Rahma Sulaiman ‘yar shekara 25 a duniya, bisa zargin da ake mata na yin garkuwa da ‘yarta mai kimanin shekara 6 a duniya, mai suna Hafsat Kabiru tare da neman kudin fansa har naira milyan 3 daga hannun tsohon mijinta Kabiru Shehu,wanda ya kasance mahaifin yarinyar.

Kwamishinan  yansandan jihar Kano, CP Usaini Muhammad Gumel  ya fadawa manema labarai cewar,  rundunar  ta samu  labarin faruwar al’amarin ne  daga  Kabiru shehu a ranar 8 ga watan Mayun da muke ciki.

Kabiru Shehu ya  fadawa  rundunar  ‘yanansandan jihar  Kano cewar, Tsohuwar  matar  tasa Rahma,  ta  gaya  masa cewar  yarinyarsa  Hafsat Kabiru ta bace, Kuma wasu mutane  sun kira  ta suna  neman  a basu naira milyan 3 a matsayin kudin fansa.

Kwamishinan yansandan jihar Kano, Ya  ce  an samu nasarar kubutar da yarinyar  a karamar hukumar Madobi dake nan jihar  kano, yayin da kuma aka cafke  mahaifiyar  tata,  inda  daga bisani ta  tabbatar da aikata lefin.

Wakilinmu Bashir  Faruk Durumin Iya, ya ruwaito mana  cewar  rundunar  ‘yansandan jihar Kanon, ta kuma samu nasarar  kama daurin tabar  wiwi har guda  605 da sauran  miyagun kwayoyi  daga  hannun wasu mutane  da ake zargi da dillancin miyagun kwayoyi, inda yanzu haka ake cigaba da bincike.