On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

'Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ma'aikacin Kotu A Jihar Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani mutum mai suna Linus Dimas dan shekara 43  da ke zaune a Kugama Wuro Jibir a karamar hukumar Mayo Belwa.

Ana zargin Dimas da kin  karbar sammacin kotu da ma’aikacin kotun yankin Nasarawo Jereng, Yauba Usman ya kai masa.

Sai dai a wani yanayi mai tada hankali, an rawaito wanda ake zargin ya daba wa Usman wuka da dama, wanda hakan ya janyo masa munanan raunuka.

Bayan an garzaya da shi asibiti, ma’aikacin kotun ya rasu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sulaiman Nguroje, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata, ya ce kwamishinan ‘yan sandan, Afolabi Babata, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan al'amarin.