On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Yan Sandan Kano Cafke Wani Mutum Kan Zargin Satar Mota

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta kama tare da bayyana wani mutum mai shekaru 51, Mahe Ibrahim, mazaunin unguwar Rijiyar Zaki, bisa zargin satar ababen hawa.

An ce lokacin da aka kama shi, an samu wata bindiga, wuka da kuma tabar wiwi a hannunsa.

Jami'an 'yan sandan Panshekara ne suka cafke wanda ake zargin a Sabon Titin Dorayi, bayan da wasu mazauna yankin suka sanar da su cewa yana ƙoƙarin satar wata mota.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar ta kuma kwato motar da ake zargin an yi yunƙurin sata, wadda babu lamba a jikin ta. 

Wakilinmu, Bashir Faruk Durumin Iya, ya ruwaito cewa Kwamishinan 'Yan Sandan ya ce bincike kan lamarin na ci gaba da gudana. yana mai tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thunder storm

    High: 33°C | Low: 23°C