On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

'Yan Ta'adda Sun Sace Wani Limamin Majami'a

Revrend Father

Yan Ta’adda sun yi awon gaba da wani Limamin Majami’a, Father Emmanuel Silas dake Majami’ar st. Charles ta mabiya darikar Katolika dake yankin Zambina a karamar Hukumar Kauru dake jihar Kaduna.

Rahoton Sace Limamin Majami’ar na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, dauke dasa hannun Revrend Friday Emmanuel Okolo.

Okolo yayi kira ga jam’ar yankin dasu kwantar hankalinsu a yayin da ake bakin kokari domin  ganin an kubutar dashi cikin koshin lafiya.

Revrend Emmanuel Silas ya shiga cikin jerin shugabannin majami’ar da aka yi garkuwa dasu a kwanan nan.