Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kogi ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace gawar wani mamaci.
Rahotanni sun rawaito cewa gawar ta marigayi Augustine Ikwue ce, jami'in Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), wanda ya rasu a Lokoja, kuma ana kan hanyar kai gawarsa zuwa Otukpo da ke Jihar Benue domin yi masa jana'iza.
Da take amsa tambayar manema labarai, jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, ASP Salisu Oyiza, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa rundunar na kan lamarin, kuma an riga an kwato gawar tare da kai ta dakin ajiye gawa na Elemona da ke Ejule.
Ta ce, "Rundunar ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar 9 ga Yulin 2026 a kan babbar hanyar Ochadamu zuwa Ejule, lokacin da wasu dauke da makamai suka kai hari kan wata motar bas kirar Hummer da ke dauke da gawar daga Lokoja zuwa yankin gabashin kasar nan, inda suka yi awon gaba da fasinjojin zuwa cikin daji."
A cewarta, nan da nan bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami'an 'yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji da kungiyoyin 'yan sa kai suka garzaya wurin tare da fara sintirin cikin daji domin aikin ceto.
Oyiza ta bayyana cewa, "Zuwa yau, an kara tsaurara aikin hadin gwiwar jami'an tsaro, inda ake ci gaba da sintirin cikin dazukan Ugbakpedo da Ofejiji, tare da kara sanya ido da sintiri a manyan hanyoyin yankin."
Ta ce ana ci gaba da kokarin ceto mutanen da aka sace tare da cafke wadanda suka aikata laifin, tana mai tabbatar wa jama'a cewa za a ci gaba da fitar da karin bayani yayin da ake samun sabbin bayanai.
Comments
Add a comment