On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Yansandan Kano Sun Cafke Wani Darakta Da Ake Zargi Da Yin Gwanjon Kayan Gwamnati

Kwamishinan 'Yansanda Kano

Kwamishinan yansandan jihar Kano, Hussaini Gumel ya tabbatar da cafke wani Darakta a Ma’aikatar samar da albarkatun ruwan shat a jihar Kano, Mai suna Abubakar Gambo, tare da wasu mutane biyu saboda samunsu da lefin yin gwanjon wasu kayayyaki mallakin gwamnati

Kwamishinan ya fadawa manema labarai a jiya cewar, Sauran mutanen biyu  sun hada da Baba Yahya wanda  ya kasance mataimakin sakataren mulki  sai kuma  Nuhu Mansir wanda ya kasance  tsohon mai kula da shirin noman rana na KAREFA a karamar  hukumar  Tudun Wada,  wadanda  suma  tuni  suka fada komar  su.

Ya zarge su  da  yin satar  saka hannu a cikin wata wasika  dake  halasta, yin gwanjon wasu manyan kayayyaki na  fanfunan samar da ruwa da  kuma Tankokin ajiyar ruwa,  wadanda kwamishinan ruwa na jihar Kano, Ali  Haruna Makoda, ya musanta bada izinin yin gwanjon kayayyakin.

Kwamishinan yansandan jihar kano, ya ce  za’a mika batun gaban  kotu, da zarar  sun kammala  bincike.