On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Yau Emefiele Ke Cika Kwanaki 6 A Hannun DSS

Dakataccen gwamnan Babban bankin kasa, Godwin Emefiele , Ya shiga rana ta shida ya na tsare a hannun hukumar tsaron farin kaya ta DSS, bisa zarginsa da daukar nauyin aikata lefukan ta’adanci, da kuma badakalar kudade.

Ana yin bincike kan dakataccen gwamnan  bankin kasar ne  ta cikin sirri, A yayin da  yau  yake shiga  rana  ta shida, tun bayan da jami’an tsaron farin kayan suka yi awon gaba  da  shi,  ba tare da anji wani karin bayani ba.

Idan  ba’a manta  ba tunda farko alaka  ta yi tsami  tsakanin  Hukumar tsaro  ta farin kaya DSS  da kuma dakataccen gwamnan babban bankin kasa,bisa zarginsa  da aikata wasu  lefuka ,  wanda  koda  a cikin watan Disambar  bara, Hukumar ta nemi umarnin kotu  ta cikin sirri  domin  cafke  shi.

Babu dai  wasu alamu dake nuni da cewar  za’a iya sakin dakataccen gwamnan bankin kasar a nan kusa,  Yayin  da  har  yanzu  hukumar  tsaron  bata  kaiga yiwa  jama’a  bayani kan binciken da take gudanarwa a kansa.