On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Yau Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar APC Na Duba Na'urar Bibas Da Aka Yi Amfani Da Ita A Zaben Gwamnan Kano

A yaune kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano zata yanke hukunci kan bukatar da jam’iyyar APC ta shigar gabanta inda take neman a bata damar duba Na’urar tantance masu zabe ta BVAS da aka yi amafani dasu a lokacin zaben gwamnan jihar Kano.

A yayin zaman kotun na jiya, Lauyan jam’iyyar APC Nuraini Jimoh SAN, Ya bukaci kotun data baiwa wadanda yake karewa damar  duba  na’urorin tantance masu zaben da hukumar zabe ta kasa  ta yi amfani dasu a lokacin zaben.

Sai dai lauyan wadanda ake kara,  Barrister E Osayomi  ye  nemi kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan kano  da  ta  yi wancakali  da bukatar da jam’iyayr ta APC ta shigar  gabanta,  inda  ya  ce  lauyan bashi da hurumin shigar da bukatar a cikin kasa da kwanaki goma  da rufe  karbar  bayanan kara.

Mai shari’a  Oluyemi Akintan Osadebay  ya saka  yau  juma’a  domin  yanke hukunci akan bukatar, kazalika ya saka ranar litinin mai zuwa  a matsayin rana  ta karshe  da za’a kammala  zaman share  fage  na  shari’ar, domin fara  zaman karar  gadan-gadan.