On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Yau Litinin 15Th Augusta Ake Cika Shekara 1 Da Kungiyar Taliban Ta Kwace Iko Da Afghanistan

Shekara daya kenan da kungiyar Taliban ta karbe iko da kasar Afghanistan, al’amarin da ya kawo karshen mulkin zababbiyar gwamnatin Ashraf Ghani da kuma kawar da dimokiradiyar da Amurka ta kafa kusan shekaru 20 bayan mamaye kasar.

A ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2021, mayakan kungiyar Taliban suka kutsa kai cikin birnin Kabul, fadar gwamnatin kasar, shekaru 20 bayan kawar da su da sojojin Amurka suka yi sakamakon harin ta’addancin da aka kai birnin New York da ake kira harin 11 ga watan Satumba.

Bayan karbe ikon da Taliban ta yi a rana mai kamar ta yau, hukumomi da kasashen duniya sun katse hulda da kasar da kuma dakile kudaden da suke taimaka wa Afghanistan da shi, abin da ya jefa kusan daukacin jama’ar kasar cikin talauci da kuma yunwa saboda rashin samun abinci mai gina jiki.

Ya zuwa yanzu babu wata kasa a duniya da ta yi shelar amincewa da gwamnatin Taliban, yayin da shugabannin kasar suka karya alkawarin da suka yi na sassauta yadda suke iko da bai wa mata yancin aiki da bai wa 'yan mata damar zuwa makaranta.

Kungiyar Taliban da ta yi alkawarin dakatar da kai hare-hare, ta zafafa hare-harenta a kan dakarun Afghanistan inda ta rika samun galaba a kansu saboda janyewar sojojin Amurka da ke taimaka musu.

A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2021, shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewar, kasar za ta janye sojoji 2,500 zuwa 3,500 da suka rage a kasar kafin ranar 11 ga watan Satumbar bara, kuma wannan sanarwa ta dada bude wa Taliban kofar ci gaba da kai hare-hare da kuma kama garuruwa, inda kafin watan Agusta ta kama akasarin manyan biranen kasar.