On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Yaune China Zata Dawo Da Bada Bizar Shiga Kasar Bayan Shade Shekara Ukku Ba'a Shiga Cikinta

Bizar kasar China

Matakin na zuwa ne,a yayin da Kasar ta ce, ta samu nasarar shawo kan cutar Korona wadda masana kimiyya ke cewa ta samo asali daga can.

China  zata  sake  dawo da bada bizar shiga cikin kasar ta  ga baki masu sha’awar  yawon  bude  ido ,tun bayan data rufe  iyakokinta  a  sakamakon annobar  sarkewar numfashi ta korona  shekara  ukku  data  gabata.
Sanarwar na zuwa  ne bayan da kasar ta samu nasarar murkushe cutar ta Korona,bayan  data  dauki  matakan kakkabe  cutar  tsawon shekaru  ukku da suka  wuce.
A jiya ne, Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen kasar  China, Ji Rong,Ya  tabbatar da cewar  kasar  zata dawo  bayar da bizar shiga  kasar ta  ga  ‘yan kasashen waje  daga  yau Laraba.
Kazalika  sanarwar  ta baiyana   cewar bizar  shiga  kasar  da aka bayar  kafin  ranar  28 ga watan Maris din  2020, amma kuma aka  kulle kasar  daga bisani,  a  halin  yanzu  zata yi  aiki  ga wadanda aka  baiwa  bizar  tunda  farko.