On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Yawan Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Tiriliyan 87

Yawan bashin da ake bin Najeriya a Kasashen waje zai kai sama da dala biliyan 51 da milyan 759, yayin da a jiya ne shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar dokoki ta kasa, domin karbo sabon lamunin dala biliyan 8 da milyan 6 da kuma Euro miliyan 100 daga kasashen waje.

Bukatar Shugaban kasar wani bangare ne na basussukan da  za’a ciwa  daga kasashen  daga shekarar 2022 zuwa 2024 domin gudanar da  muhimman aiyukan  raya kasa, kamar wutar lantarki da samar da  hanyoyi da inganta samar  ruwa da shimfida  layin dogo da kuma bunkasa fannin kiwon  lafiya.

A cewar  ofishin kula da ciwo  basussuka  na kasa, yawan bashin da ake bin kasar  nan zuwa watan Yunin da  ya  gabata, ya kai dala biliyan 43 da milyan 159, yayin da bashin cikin gida ya kai Naira tiriliyan 54 da bilyan 130.

Zuwa yanzu  jimillar bashin da ake bin Najeriya na cikin  gida da kasashen waje ya kai Naira tiriliyan 87 da bilyan 379.