On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Yawan Bashin Najeriya Ya Zarce Naira Trilliyan 87.38 A Zango Na 2 Shekarar 2023 - Rahoton DMO

Ofishin kula da basussuka na Najeriya ya ce jimillar bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira trilliyan 87.38  a karshen zango na biyu na shekarar 2023.

Adadin ya nuna karuwar kashi 75.29 ko kuma Naira trilliyan 37.53 idan aka kwatanta da Naira trilliyan 49.85tn da aka samu a karshen watan Maris na 2023.

Ofishin a wani rahoto da ya fitar a ranar Alhamis ya ce bashin ya hada dana babban bankin Najeriya da yake cigaba da baiwa gwamnatin tarayya Na triliya 22.71.

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, sauran kari a kan basussukan, wasu sabbin rance ne na gwamnatin tarayya da na kananan hukumomi  daga gida da waje.