On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Yawan Mutanen Da Suka Harbu Da Cutar Kyandar Biri A Najeriya Ya Kai 140

Cutar Kyandar Biri

A yanzu haka yawan mutanen da suka harbu da Cutar Kyandar Biri a kasar nan sun kai 141 a maimakon 110 da aka samu a lokacin baya, kamar yadda cibiyar Dakile yaduwar Cututtuka ta kasa ta baiyana.

Cibiyar ta baiyana haka ne  ta cikin wani sabon rahoton data wallafa kan halin da ake ciki game  da cutar Kyandar Biri, Yace  daga  ranar 6 zuwa  12 ga  watan da muke ciki, an samu sabbin mutane 31 da suka harbu da cutar a jihohi 13.

Jihohin sun hada da Legas mai 5 sai Katsina  da Ondo da Bayelsa  masu hurhudu kowannensu, Yayin da Nasarawa keda 3 sai ogun itama mai 3 Yayin da Oyo keda 2, Sai kuma jihohin Akwa ibom da Delta da Edo da jihar Kaduna da Nan Kano da  kuma Imo masu dai-dai.