On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Za Mu Gana da INEC Kan Batan Dabon Gwarzo a Jerin Yan Takarkari - Kofarmata

Jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Dakta Yusuf Kofar Mata, ya ce Jam’iyyar  (NDC) za ta gana da jami’an hukumar INEC a Abuja yau, domin tattauna batun rashin sunan dan takarar ta na gwamnan Kano a jerin sunayen yan takara na karshe da ta fitar gabanin zaben 2027.

Da yake zantawa da wakilinmu Nura Haruna Mudi a daren jiya, dan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar birni a nan, ya bukaci mambobin jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa yana da yakinin cewa kuskuren dan adam ko kuma na na'ura ne ya jawo wannan matsala.

Dakta Kofar Mata ya jaddada cewa dan takarar gwamnan jam’iyyar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya cika dukkan sharuddan tsayawa takara bisa ka’idojin hukumar zabe ta INEC.

Ya kuma yi zargin cewa lamarin ya nuna jam’iyyar APC mai mulki na tsoron fuskantar tsohon mataimakin gwamnan Kano, Gwarzo, a zaben shekara mai zuwa.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 38°C | Low: 21°C