On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Za'a Binne Ha'korin Tsohon Firiyiministan Congo Patrice Lumumba.

Patrice Lumumba

Yau Alhamis ne za'a binne Hakorin tsohon Firiyiministan Congo, Patrice Lumumba.

Yau Alhamis gwamnatin Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo, ke gudanar da taron binne jagoran kasar na farko bayan samun 'yancin kai, Patrice Lumumba, a babban birnin kasar Kinshasa.

Hakorin na zinare shi kadai ne ya rage a wani abu na jikin firaministan kasar na farko, wanda 'yan a-waren kasar tare da hadin kan sojojin haya na kasar Belgium suka hallaka a ranar 17 ga watan Janairu na 1961.

An narkar da gawarsa ne da ruwan batir, amma kuma wani dan-sandan Belgium, kasar da ta yi wa Kongon mulkin mallaka, ya adana hakorin a matsayin wani abin tunawa.

A makon da ya gabata ne aka mayar wa da iyalan tsohon shugaban, hakorin a wani biki da aka yi a babban birnin Belgium, Brussels.

An kewaya da hakorin wanda ke cikin wani akwatin gawa da aka nade da tutar kasar ta Kongo, inda aka kewaya da shi sassan kasar da dama domin ba wa jama'a damar girmama shi da kuma ban-kwana.