On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Za'a Cigaba Da Fuskantar Rashin Wutar Lantarki Saboda Yajin Aiki

KEDCO

Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.

Wata sanarwa da  shugaban  sashin  sadarwar  kanfanin, Sani Bala  Sani  ya  fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya  ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa  na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.

Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin,  Ta baiyana cewar  za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar  yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a  yau  Laraba.

Shima  mataimakin shugaban kungiyar kwadago  ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared  Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.