On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Za'a Dauki Sabbin Malaman Makaranta Dubu 10 A Jihar Kaduna

GWAMNA EL-RUFAI

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Ya amince da daukar sabbin Malaman Makaranta Dubu 10 , wadanda zasu yi aiki a karkashin Hukumar Ilimin Bai Daya ta jihar.

Wata sanarwa da shugaban Hukumar, Tijjani Abdullahi ya fitar, Yace  tuni hukumar ta bawa  Jami’ar jihar Kaduna  damar tsara  manhajar internet  da  za’a yi amfani da ita wajen daukar  bayanan masu neman aikin, inda shafin zai fara aiki daga ranar  21 ga watan da muke ciki.

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta jihar Kaduna, Yace wadanda suka cancanci su nemi aikin koyarwar sune, masu shaidar  takardar Malanta ta NCE ko kuma digiri a bangaren ilimi da suka fito daga makarantun da aka tabbatar da ingancinsu.

Ya kara da cewa wadanda suka cike bayanan nasu, zasu je dauke da takardunsu na ainihi domin tantancewa, sannan kuma daga bisani wadanda suka samu nasara, hukumar Ilimin Bai Daya ta jihar  zata wallafa sunayensu .