On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Za'a Dawo Da Zirga-Zirgar Jirgin Kasa Daga Kaduna Zuwa Abuja A Ranar Litinin Mai Zuwa.

JIRGIN KASA

Matukar ba wani sauyi aka samu ba, za’a dawo da sufurin jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin 28 ga watan Nuwambar da muke ciki.

Wannan na zuwa ne watanni takwas bayan dakatar da zirga-zirgar jiragen kasar saboda harin da 'yan ta'adda suka kai a a ranar 28 ga watan Maris din bana, inda aka yi garkuwa da mutane da dama tare da kashe wasu guda  takwas.

Wata majiya a tashar jirgin kasa ta Idu ta shaida wa jaridar Punch a Abuja cewa za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen a ranar Litinin mai zuwa. A cewar majiyar, wasu ‘yan kwangila da aka dauka, sun saka kyamarorin tsaro da kuma mai bayar da bayanai.