On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Za'a Fara Aikin Rushe Gine-gine Dake Kan Magudanan Ruwa A Kasuwar Kantin Kwari - Gwamnatin Kano

Majalisar zartaswa ta jihar Kano ta bada umarnin sanya alama tare da rushe duk wasu gine-ginen da akayi a kwarin Gogau dake tsakiyar birni.

Har ila yau, sauran wuraren da wannan aiki na rusau zai shaf sun hadar da layukan magudanun ruwa a cikin da kewayen Kasuwar Kantin Kwari da nufin tabbatar da fitowar ruwa daga kasuwar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba shine ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon taron majalissar zartaswa na mako-mako da akayi ranar Laraba.

Yayin da ta ke karbar rahoton ambaliyar ruwa a kasuwar Kanti Kwari, majalisar ta kuma ba da umarnin a cire duk wasu gine-gine ko tebura na wucin gadi da aka dora a saman magudanan ruwa a cikin kasuwar da kewaye.