On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Za'a Fara Amfani Da Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro Ta R21 A Najeriya

R21

Gwamnatin tarayya ta ce za a fara amfani da Rigakafin zazzabin cizon sauro ta R21 a kasar nan nan da watan Afrilun 2024.

 Ministan lafiya, Dr . Osagie Ehanire  shi ne ya bayyana haka a  jiya   yayin wani taron manema labarai da aka shirya a Abuja, a wani bangare  na ranar  yaki da zazzabin cizon sauro ta duniya.

Ministan wanda babban sakataren ma’aikatar, Mamman Mamuda ya wakilta ya ce Najeriya ta nemi   samun rigakafin  har  sau ukku a jere.

Ya ce ma’aikatar tana aiki kafada da kafada da hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki wajen tsara dabarun rarraba  rigakafin zazzabin cizon sauro.

 

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 37°C | Low: 23°C