On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Za'a Fuskanci Daukewar Lantarki Sakamakon Yajin Aikin Da Ma'aikatan Lantarki Zasu Fara A Yau Laraba

Ma'aikatan Lantarki suna tsaka da yin Gyaran Wuta

A yayin da ake fuskantar barazanar tafiya yajin aiki daga bangaren Ma’aikatan wutar lantarki a kasar nan, A yanzu haka kanfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa TCN, Ya roki Ma’aikatan dasu maida wukarsu cikin Kube, kada su fara yajin aikin da suka yi niyyar somawa daga yau.

Shugaban Kanfanin Dr Sule Abdulaziz  ne yayi wannan roko ta ciki wata wasika da aka aikewa ma’aikatan Lantarkin, biyo bayan barazanar da suka yi na tsayar da aiyukansu cak, muddin aka ki biya masu bukatunsu.

 

Ma’aikatan dake karkashin Hadaddiyar kungiyar Ma’aikatan lantarki ta kasa, Ta umarci daukacin ‘ya’yanta dasu rufe  dukkanin rassan  ofisoshin kanfanin samar da lantarki na kasar nan, sannan kuma su  fara yajin aiki daga yau.

 

Babban sakataren kungiyar, Mister Joe Ajaero, Yace  daukar matakin rufe ofisoshin kanfanin, nada alaka da ganin sun nuna bacin ransu, kan umarnin da hukumar gudanarwar kanfanin ta bayar, na cewar  dukkanin Mu’kaddasan Daraktoci  dake son zama  cikakkun Daraktoci ya zama  wajibi su rubuta jarabawa, wanda kuma yin haka ya ci karo da tsarin aikinsu.

 

Kazalika ma’aikatan sunyi korafin yadda gwamnatin taraiyya ta gaza  biya tsaffin ma’aikatan rusasshen kanfanin samar da wutar lantarki na kasa PHCN hakkokinsu tun daga watan Disambar shekarar   2019.