On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Za'a Fuskanci Mamakon Ruwan Sama A Jihohin Kano Da Legas Da Wasu Jihohi 17

MAMAKON RUWA SAMA

Za’a fuskanci mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu jihohi 19 na arewaci kasar nan daga tsakanin watan Augusta zuwa Oktoban kamar yadda hukumar Kula da Yanayi ta kasa ta baiyana .

Hukumar ta baiyana  cewa  jihohin da za’a fuskanci  mamakon ruwan sun hada  da nan Kano sai Sokoto da Zamfara da katsina da Jigawa da Yobe sai Borno da Bauchi  da Kebbi da Gombe da kuma kaduna da jihar Adamawa.

Shugaban hukumar Mansur Matazu  ya fadawa manema Labarai a Abuja cewa, Na sane da irin mamakon ruwan sama da aka fuskanta kwanan-nan a wasu daga cikin jihohi, wanda  hakan baya rasa nasaba da sauyin yanayi da aka samu, kamar yadda hukumar tayi hasashe a baya.

Ya kara da cewa Hukumar zata  cigaba da yin hasashe  kan yadda  ruwan sama zai kasance a mabanbantan wurare dake kasar nan.