On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Za'a Fuskanci Mamakon Ruwan Sama A Kano Da Wasu Jahohi 20

RUWAN SAMA

Hukumar kula da yanayi ta kasa, Ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama kamar dab akin kwarya a wasu bangarori na jahohin Kano da Kwara da Niger a yau Juma’a da kuma ranar Asabar, Yayin da kuma za’a samu matsakaicin ruwan sama a wasu jahohin kasar nan guda 20.

Bayanin hakan na kunshe  ne cikin rahoton hasashen yanayi da hukumar  ta fitar  a ranar Alhamis.

Rahoton ya baiyana  cewar, za’a iya  fuskantar mamakon ruwan sama a cikin sa’oi 24, sannan kuma wasu wuraren za’a samu matsakaicin ruwan sama, yayin da  za’a  iya  fuskantar  tumbatsar  koguna  da  zaizayar kasa, da kadawar iska mai karfi  da  Cida  da kuma  tsawa.

Hukumar kula da yanayin ta kasa ta baiyana cewar jahohin da za’a iya fuskantar matsakaicin ruwan sama a gobe Asabar,  sun  hada  da wasu bangarori na jihar Ribas sai Delta da Bayelsa da AKwa Ibom da Cross River da  Yobe.

Sauran sune Benue  da Jigawa  da Katsina sai Zamfara  da kuma jahar  Sokoto.