On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Za'a Kammala Aikin Titin Kaduna Zuwa Kano Kafin Ranar 29 Ga Watan Mayu 2023 - Fashola

Gwamnatin tarayya ta ce za a kammala aikin titin Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano kafin ranar 29 ga watan Mayu.

Ministan ayyuka da gidaje, Mista Babatunde Raji-Fashola, SAN, shine ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin da ya ke duba aikin babbar hanyar.

Bangaren babbar hanyar na daga cikin aikin da ya kai kilomita 375.4 daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano da aka bayar a lokacin mulkin Buhari na farko.

Ya ce za a kammala sashen kuma za a bude shi kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar mulki a watan Mayu.

Fashola ya ce yayin da aka kusa kammala kashi na biyu da na uku wanda ya kai kilomita 210, sashe na daya daga Abuja zuwa Kaduna za’a barwa gwamnati mai jiran gado.