On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Za'a 'Kara Farashin Burodi

Burodi

Farashin Burodi zai tashi a sakamakon tsadar Sikari da Fulawa a Najeriya

Jaridar Punch ta ruwaito ƙungiyar masu sana'ar saida Buredi ta kasa na cewa farashin fulawa da sikari da sauran kayan haɗi da ake amfani da su wurin yin biredi duk sun yi tashin gwauron zabi.

Ƙungiyar ta kuma ƙalubalancin gwamnatin Najeriya kan zargin nuna halin ko in kula dangane da wannan batu inda ƙungiyar ta yi barazanar tafiya yajin aiki daga ranar 13 ga watan Yulin 2022.

Ko a kwanakin baya dai sai da aka ƙara kuɗin biredi a Najeriya sakamakon ƙarin farashin kayayyaki.