On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Za'a Karrama Tinubu Da Lambar Karramawa Ta GCFR

TINUBU

A ranar Alhamis mai zuwa ce, Za’a karrama zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da lambar girmamawa ta kasa GCFR, da kuma mataimakinsa Kashim Shettima wanda za’a bashi lambar girmamawa ta GCON.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai jagoranci bukin bada lambobin karramawar.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Hadimin shugaban kasa  ta bangaren kafafen sada zumunta, Tolu Ogunlesi  ya  fitar.

Kazalika sanarwar  ta baiyana cewar a ranar ne kuma za’a mika  kundin bayanan mika  mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa.