On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Za'a Kori Shirin AGILE Daga Katsina

SARKIN KATSINA

Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir, Ya baiyana aniyarsa na kawo karshen shirin nan dake bada tallafi wajen bunkasa ilimin ‘ya’ya mata mai suna AGILE a cikin jiharsa ta Katsina.

Sarkin ya baiyana cewar shirin  ya saba da tanadin koyarwar  addinin musulunci da kuma  al’adun  mutanen yankin arewa, wanda  hakan ke zama wata makarkashiya ga iyaye  da kuma  al’ummar  gari.

Ya ce  ya zama wajibi a dauke shirin na AGILE daga  jihar Katsina, kuma ba zai lamunci duk wani  tsari da zai zama katsalandan ga tafarkin  koyarwar ilimin da ake kanta a halin yanzu ba.

Idan ba’a manta ba, Koda a nan kano, wata kungiyar farar hula mai suna Kungiyar Matasan Kano, ta roki gwamnan Kano Abba Kabir  Yusuf da ya kafa kwamitin bincike  domin gano wasu zarge-zarge na boyayyiyar manufar dake shirin  na AGILE, wanda  yanzu haka ke gudana a wasu makarantu na jihar Kano domin yin gyaran  da  ya da ce.