On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Za'a Rika Cin Tarar Masu Wulakanta Tutar Najeriya Naira Dubu 100

TUTAR NAJERIYA

Majalisar wakila na wai yunkuri domin kara yawan tarar da ake ci kan wadanda aka samu da lefin wulakanta Tutar Najeriya daga naira 100 zuwa naira dubu 100.

A jiya ne kudirin yin gyara kan girmama Tutar Najeriya  ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar  wakilan.

Dan majalisa  Sada Soli na jam’iyyar APC daga jihar Katsina wanda ya gabatar da kudirin, ya ce  ana samun daidaikun al’umma da kuma  jama’ar gari da  wasu kungiyoyin dake cikin wulakanta tutar  Najeriyar.

Da yake  yanke hukunci kan kudirin, Mataimakin shugaban majalsiar  Benjamin Kalu  ya mika kudirin gaban kwamitin majalisar daya  da ce domin daukar mataki na gaba.